?ungiyar likitoci masu lura da lafiyar mata ta ?asa ta bu?aci shugaban ?asa Muhammadu Buhari da ya sanya hannu kan dokar kare lafiyar mata da jarirai.
A cewar ?ungiyar hakan zai zamo wani abin tarihi, wanda al’ummar ?asar ba za su manta da shi ba.
Shugaban ?ungiyar, Dr Habib Sadauki ne ya bu?aci hakan a wata ganawa da ya yi da manema labarai ranar Lahadi.
Sadauki ya ce dokar za ta taimaka wajen rage mutuwar mata masu juna-biyu da jarirai.
Ya ?ara da cewa Najeriya na daga cikin ?asashen da har yanzu suke da mafi yawan al?aluma na mace-macen masu ciki da kuma jarirai.
