Rahotanni daga Jihar Delta na bayyana cewar wani abin mamaki ya faru a kauyen Oghara da ke Jihar inda aka tsinci gawar wani mutum bisa wata matar aure yana tsakiyar lalata da ita.
Rahotanni sun bayyana mutumin mai suna Victor da cewar sanannen Maharbi ne a kauyen kuma amini ne wajen mijin matar da ya mutu a kanta.
Matar mai suna Julie ta samu sabani da mijinta ne lamarin da ya kai su ga rabuwa, inda Mijin ya nemi alfarma wajen Victor da ya taimaka yayi mishi biko, inda Victor ya yi amfani da wannan dama wajen gyara wa kanshi hanya.
