Kanawa Sun Fi Gamsuwa Da Hisbah Akan ‘Yan Sanda – Shekarau

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar Dattawa kuma tsohon gwamnan jihar kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce mazauna jihar sun fi yadda da samun natsuwa da jami’an Hisbah a kan jami’an ‘yan sanda a fadin Jihar.

Shekarau ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba. Inda ya jaddada bukatar samar da ‘yan sandan yanki domin shawo kan matsalar tsaron da ya addabi kasar nan musanman yankin Arewa.

“Tsaro alhakin kowa ne kuma hakan yasa ake bukatar ‘yan sandan yanki,” yace.”A cikin shekara daya zuwa biyu da aka samar da hukumar Hisbah, mun yi nasarar shawo kan kusan kashi 90 na matsaloin da ke damun al’ummarmu kuma mun samu zaman lafiya.

Tabbas wannan na daga cikin abinda Kano ke jin dadi yanzu. “Ka tambaya kowa a Kano yau, jama’a sun fi son zuwa ofishin Hisbah domin kai rahoton duk abinda ya faru a al’umma fiye da zuwa wurin ‘yan sanda ko kuma kotu.”

Sanata Ibrahim Shekarau shi ya kirkiro Hukumar Hisbah a Jihar Kano zamanin mulkin shi a jihar daga Shekarar 2003-2011, da niyyar daidaita al’amurra a fa?in jihar mafi yawan jama’a a yankin Arewa.

Related posts

Leave a Comment