Lafiya: An Samu Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta amince da a fara bayar da wani riga-kafin zazzabin cizon sauro.

Wannan shi ne riga-kafin na Malaria na farko da aka amince da ingancinsa a duk fadin Duniya.

A kasashen Afirka za a fara raba riga-kafin wanda kamfanin GlaxoSmithKline na kasar Birtaniya ya kirkiro.

Malaria zazzabi ne wanda ke kashe akalla mutum 400,000 a duniya a kowace shekara, amma ya fi addabar kasashen Afirka.

Related posts

Leave a Comment