Rahotanni dake shigo mana daga babban birnin tarayyaAbuja na bayyana cewar Babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja ta yanke wa Faisal, dan gidan AbdulRasheed Maina, tsoohon shugaban hukumar fansho, hukuncin shekaru 14 a gidan gyara hali.
Alkali Okon Abang, wanda ya yanke hukuncin ya kama Faisal Maina da laifuka uku da hukumar EFCC ta zargesa da shi.
Har yanzu ana cigaba da shari’ar mahaifin nashi bayan samun shi da aikata ba daidai ba a wasu ma?udan ku?a?e na ma’aikatar fansho ta kasa.
