Kwamishinar Zamfara Ta Aje Aiki Domin Mukamin Kwamishina A Jihar Imo

Kwamishiniyar Mata da Yara ta Jihar Zamfara, Rabi Shinkafi ta yi murabus domin kar?ar mu?amin kwamishina a Jihar Imo.

Da ta ke baiyanawa Kamfanin Daillancin Labarai na ?asa, NAN, Shinkafi ta ce “Na yi murabus a matsayin Kwamishiniya a Zamfara domin kar?ar wani mu?amin a Imo.

“ina mai matu?ar godiya ga Gwamna Bello Matawalle da mai ?akin sa, Hajiya A’isha Matawalle saboda alherin da su ke nuni da kuma bani damar yi wa Zamfara hidima a ?angarori daban-daban.

“Duk wasu ra?e-ra?i da a ke yi a kan murabus dina ?arya ne, aikin ?an sharri ne . Ni akwai kyakkyawar ala?a tsakani na da gwamna da mai ?akin sa.

“Da shi gwamnan Imo Hope Uzodinma da Matawalle sun tattauna a kan mu?amin nawa kuma dukkan su dai ?an jam’iyar APC ne,” in ji Shinkafi.

Related posts

Leave a Comment