Shugaban Hukumar za?e mai zaman kanta Farfesa Mahmood Yakubu ya ro?i al’ummar Najeriya su taimaka wurin kare kadadrorin hukumar gabanin babban za?en ?asar mai zuwa.
Hakan na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai wa wasu ofisoshin hukumar a baya-bayan nan.
Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da ?ungiyar dattijan yammacin Afirka, a ofishinsa da ke Abuja, a ranar Litinin.
Shugaban na INEC ya ce babban abin da ake fargaba gabanin za?en mai zuwa shi ne matsalar tsaro.
Ya ce “an kai hari a ofisoshinmu a ?ananan hukumomi uku, a cikin ?asa da mako uku, irin wa?annan hare-hare guda bakwai ke nan aka kai a cikin wata hu?u.”
Ya ?ara da cewa “nauyi ne a kanmu baki ?aya mu ha?a hannu domin kare su. Dole ne a daina kai hare-haren kuma wajibi ne a kamo tare da gurfanar da masu alhakin kai harin.”
Sai dai ya tabbatar wa al’umma cewa za a gudanar da za?en kamar yadda aka tsara, duk da barazanar tsaro da ake fuskanta.
