Kotu Ta Yi Fatali Da Bukatar Gwamnati Na Mika Kyari Amurka

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya ta yi watsi da ?arar da gwamnatin tarayya ta shigar ta neman a tasa ?eyar Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ?an sandan da aka dakatar saboda zarginsa da kar?ar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi zuwa Amurka.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi fatali da ?arar da Ministan shari’a, Abubakar Malami, ya shigar bisa dalilin cewa ?arar na da na?asu.

A watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari bisa zargin kar?ar cin hanci daga Hushpuppi – mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.

Kyari na cikin zaratan jami’an ‘yan sandan Najeriya da suka yi fice wajen yaki da miyagun laifuka a kasar, yayin da wannan batu na cin hanci da rashawa ya haifar da cece-kuce a sassan kasar.

Related posts

Leave a Comment