Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya mika sakon jaje ga mutane sama da 500,000 da ambaliya ruwa ta shafa a fadin kasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya alkawarta cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bayar da taimakon gaggawa ga wadanda iftila’in ta shafa.
Ya kuma yi kira ga daidaikun masu hannu da shuni da kungiyoyi da su taimaka wa dubban mutanen da lamarin ya shafa.
Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwwar gwamnatocin jihohi, za su yi aiki tare wajen rage barnar da ambaliyar ta yi.
Haka kuma sanarwar ta ambato shugaban na kira ga mazauna wuraren da ka iya fuskantar ambaliya da su rika amfani da gargadin farko da hukumomi ke yi musu game da yiyuwar afkuwar ambaliyar.
An dai samu rahotonnin ambaliya ruwa a jihohin Legas, da Yobe, da Borno, da Taraba, da Adamawa, da Edo, da Delta, da Kogi, da Niger, da jihar Plateau.
Sauran sun hadar da Benue, da Ebonyi, da Anambra, da Bauchi, da Gombe, da Kano, da Jigawa, da Zamfara, da Kebbi, da Sokoto, da Imo, da kuma jihar Abia, tare da babban birnin kasar Abuja, inda lamarin ya shafi mutum 508,721, tare kuma da raba sama da mutum 73,379 da muhallansu.
Yayin da aka samu rasa rayuka 115 , sannan kuma mutum 277 suka samu raunuka.
Sanarwar ta kuma ce gwamnati ta samu rahotonnin da ke cewa gidaje kusan da 37, 633 ne suka zube sakamakon ambaliyar.
