Tsaro: Pantami Ya Bada Umarnin Rufe Layukan Waya Marasa Lambar Katin Dan ?asa

Gwamnatin tarayya ta bada umurni ga dukkan kamfanonin sadarwa su rufe layin wayan wanda bai hada layinsa da lambar katin zama dan kasa nan ba nan da ranar 30 ga Disamba, 2020.

Wannan Umarni ya biyo bayan ganawar gaggawan ta masu ruwa da tsaki a sashen sadarwa da Minista, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami ya shirya ranar Litinin, 14 ga Disamba, 2020 a birnin tarayya Abuja.

Bayan ganawar, an yi ittifakin cewa tun da fari daga ranar Alhamis, 16 ga Disamba, 2020, dukkan kamfanonin sadarwa su bukaci mutane su hada layukan wayansu da lambar katin zama dan kasa domin tantancewa.

A wani cigaba da aka samu Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis tace an rage kudin ‘Data’ da kashi 50% bisa umurnin da aka baiwa hukumar sadarwan Najeriya NCC. Saboda haka, kudin ‘Data’ na 1GB ya sauko daga N1000 zuwa N487 daga yanzu ( tun watan Nuwamba).

‘Data’ kudi ne da mutum ke saya domin amfani da samun shiga yanar gizo. Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami, wanda ya sanar da hakan ya ce, an yi hakan ne bisa umurnin da aka ba hukumar NCC na tabbatar da cewa an rage kudin ‘data’ a fadin tarayya.

Related posts

Leave a Comment