Hukumar Lafiya Ta Duniya ta bayyana cewa tana da ya?inin cewa za a magance annobar korona a shekarar 2022 matu?ar ?asashe suka ha?a kansu suka yi aiki kafa?a da kafa?a.
Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan inda ya ce a halin yanzu akwai abubuwan da ake amfani da su domin kare kai da kuma maganin korona amma a cewarsa, i?irarin kishin ?asa da kuma ?oye rigakafi da wasu ?asashe ke yi ne ya haddasa ?ullar sabon nau’in Omicron na korona.
Mista Tedros ya bayyana cewa idan aka ci gaba da nuna bambanci, akwai barazanar cewa cutar za ta ci gaba da sauyawa ta hanyoyin da ba a yi zato ba.
