Tun bayan da bayanai suka fito daga babban bankin Najeriya cewa ya kori ma’aikata 117, masu manyan matsayi, ‘yan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta suke ta tofa albarkacin bakinsu.
Yayin da wasu ke alakanta abin da kabilanci ko bangaranci da dama na nuna cewa addinanci ne ya yi tasiri.
Hakan ne ya sa BBC ta tambayi wasu ma’aikatan babban bankin wadanda ‘yan arewacin kasar ne da ake ganin an dauki matakin domin su.
BBC ta gano cewa CBN na gudanar da bincike ne ta ?ar?ashin ?asa tare da ?aukar mataki kan dukkan wa?anda aka kama da hannu kan zargin da ake musu na aikata ba daidai ba.
Ba dai lokaci guda bankin ya kori ma’aikatan nasa ba da a yanzu suka haura 100.
Amma da korar mutum 50 da ya yi na baya-bayan nan, adadin kamar yadda bayanai ke cewa ya kai 117.
Mutanen da BBC ta tattauna da su daga CBN din sun bayyana mata cewa korar ta shafi wasu manyan sassa uku ne na bankin da suka hada da ?angaren ba da tallafi wanda a turance ake cewa (Intervention) da mai kula da kwantaragi ko kuma procurement a turance da kuma mai kula da harkar lafiya wato medical department.
Majiyoyin BBC sun tabbatar da cewa “an tafka badakala a babban banki a shekarun da suka gabata.”
A ?ar?ashin sashen bayar da tallafi ne dai CBN ya gudanar da shirye-shirye irin na ba da rance ga manoma na Anchor Borrowers da bayar da rance na Korona dai sauransu da aka gudanar lokacin gwamnatin Buhari.
A baya-bayan nan ne babban bankin ya sanar da cewa har yanzu kudade fiye da biliyan 500 sun makale a hannun jama’a ba su koma wa bankin ba.
