Kisan Zamfara: Buhari Ya Tura Wakilai Yin Jaje

Labarin dake shigo mana daga Jihar Zamfara na bayyana cewar Wakilan gwamnatin tarayya sun dira Gusau, babban birnin jihar ranar Laraba, domin jajantawa gwamnatin jihar bisa harin yan bindiga na kwanan nan.

An ruwaito cewa tawagar wakilan karkashin jagorancin Ministan tsaro, Bashir Magashi, ta kunshi, ministan ayyukan jin kai, Sadiya Umar Farouq, da kakakin Buhari, Malam Garba Shehu. Sauran mambobin tawagar sun ha?a da, ministan harkokin yan sanda, Muhammad Dingyadi, mai bada shawara kan tsaro, Babagana Monguno, da kuma Sufeta janar na yan sanda, Usman Baba.

Idan masu karatu za su tunawa kwanakin baya ne wasu tsagerun yan bindiga ?auke da muggan makamai suka kai mummunan hari kauyukan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum dake jihar ta Zamfara, inda suka karkashe mutane masu yawa.

An samu banbancin adadin mutanen da aka kashe yayin harin, amma gwamnatin Zamfara tace mutanen da aka kashe sun wuce 50. Saidai wasu majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun halaka mutane sama da 200 yayin mummunan harin.

Related posts

Leave a Comment