Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta ceto yara sama da dari daya da take zargin ana azabtar da su a wani gidan mari da ke birnin Kano.
‘Yan sandan sun ce sun ceto yaran ne da shekarunsu suka kama daga 4 zuwa 10, bayan sun sami koke daga wasu daga cikin daliban makarantar da suka gudu lokacin da aka tafi binne daya daga cikinsu da suke zargi dan mai makaranatar ne ya yi sanadiyar mutuwarsa ta hanyar azabtarwa da duka.
A hirarsa da BBC, kakakin rundunar ‘yan sandan na Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce: ”Wasu matasa ne su goma wadanda shekarunsu suke tsakanin 10 zuwa 14 suka je hedikwatar ‘yan sanda inda suka shigar da korafi a kan wani mutum da yake gudanar da makarantar mari ba bisa ka’ida ba, wadda daga can suka gudo, mutumin mai suna Musa Safiyanu dan kimanin shekara 55 da ke unguwar Na’ibawa ‘yan-lemo, karamar hukumar Kumbotso a nan Kano.”
Ya kara da cewa: ”Sun ce a wannan gida nasa akwai yara sama da dari wasu an daure su wasu kuma an kulle su a dakuna wanda da daya ya yi laifi aka dinga dukansa, dan gidan mai gudanar da makarantar shi ya yi dukan wanda dukan yayi sanadiyyar mutuwar daya daga cikinsu.”
SP Kiyawa ya ce yaran da aka samu a makarantar su 113 ne, inda aka tarar da su a yanayi na azabtarwa da rashin kyawun wurin kwana da abinci, sannan ba abincin da ake ba su sai tuwo safe da rana.
