Bamu Ga Amfanin Kulle Layukan Sadarwa A Sokoto Ba – Tambuwal

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Gwamnan Jihar Aminu Waziri Tambuwal ya nemi gwamnatin tarayyar Najeriya ta janye matakin da ta ?auka na rufe layukan sadarwa a jiharsa sakamakon hare-haren ‘yan fashin daji a yankin.

Cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan kafofin ya?a labarai, Muhammad Bello ya fitar ranar Asabar, Gwamna Tambuwal ya rubuta wa gwamnatin wasi?a ne yana neman a ?age rufewar da aka yi wa layukan sadarwar.

Tun a watan Satumba ne hukumar sadarwa ta ?asa NCC ta rufe layukan salular a ?ananan hukumomi 14 na Sokoto da kuma wasu yankunan a jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara.

“Tambuwal ya ce ya nemi a janye matakin ne saboda damuwar da jami’an tsaro suka nuna cewa rashin layin sadarwa na kawo musu cikas wajen gudanar da ayuukansu,” a cewar sanarwar.

Tambuwal ya bayyana hakan ne lokacin da yake kar?ar ba?uncin Gwamna Umara Zulum yayin da ya kai ziyarar jaje game da harin da ‘yan fashi suka kai a Gwaranyo, inda suka kashe mutum 43.

Related posts

Leave a Comment