Hukumar ?akile cutuka masu ya?uwa a Najeriya ta ce cutar kwalara na ci gaba da ya?uwa a a Najeriya inda aka samu ?aruwar ya?uwar cutar da kashi 44.
Rahoton da hukumar ta fitar ranar Litinin ta ce cutar ta kashe mutum 30 a mako ?aya a jihohin Bauchi da Katsina da Neja da Jigawa da kuma Abuja.
Cutar ta fi yin kisa a jihar Bauchi inda mutum 11 suka mutu a mako ?aya, Katsina mutum 10 sai Neja mutum 6 da kuma Abuja mutum ?aya.
Sannan mutum 1,162 suka kamu a johohi bakwai cikin mako ?aya da suka ha?a da Bauchi da Katsina da Neja da Jigawa da Kano da Borno da Adamawa da kuma Abuja.
Al?alumman hukumar sun nuna cewa mutum 816 suka mutu sakamakon kwalara a jihohi 22 da Abuja tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2021.
Rahoton ya ce cutar ta fi kama yara daga shekara biyar zuwa 14.
