Wata babbar kotun jihar Jigawa da ke zamanta a Gumel ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani magidanci mai suna Rabiu Mamman.
Mutumin mazaunin kauyen Medin Labo a karamar hukumar gagarawa kotu ta yanke masa wannan hukuncin ne bayan samun shi da laifin kashe matarsa.
Alkalin kotun, Justice Abubakar Mohammed Sambo, ya ce kotu ta tabbatar da wannan hukuncin bayan shaidu da bayanai sun tabbatar, Mamman ya kashe matarsa a daji.
A cewar sanarwar da kakakin ma’aikatar shari’a ta fitar, Zainab Baba Santali, a shekarar 2016 mutumin ya aikata laifin, lokacin da ya ka?a matarsa daji sannan ya yi amfani da sanda ya rafka mata a kai, nan take rai ya yi halinsa. Sannan ya ha?a rami ya binne ta.
