Ofishin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kashe Naira Biliyan 2.42 a kan tafiye-tafiye na cikin gida da kasashen ketare a 2021 yayin da fadar shugaban kasa za ta kashe Naira Miliyan 135.6 a kan lemuka kamar yadda ya ke rubuce a cikin kasafin kudin bana.
A ranar 31 ga watan Disamban 2020 ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan kasafin kudin kasar nan na 2021. A kasafin kudin, jimillar kudin da aka warewa ofishin shugaban kasan na manyan ayyuka shine N3.82bn sai N2.76bn na ayyukan yau da kullum.
Sauran abubuwan da ke cikin kasafin kudin na 2021 shine kayan abinci da sauran kayan girki na ofishin shugaban kasan zai kwashe Naira Miliyan 98.3, alawus na zama zai lashe Naura Miliyan 164.17 yayin da Naira Miliyan 41.21 za ta tafi wurin talla da hulda da jama’a.
A ofishin mataimakin shugaban kasa, za a kashe Naira Miliyan 801.03 na tafiye-tafiyen cikin gida da kasashen ketare, lemuka da abinci za su lashe Naira Miliyan 18.26, alawus na zama zai kwashi Naira Miliyan 20.26.
An ware Naira Miliyan 50.88 miliyan domin samar da kayan abinci da na hadinsu sai kayayyakin walwala za su kwashe Naira Miliyan 23.
Ofishin zai kashe Naira Miliyan 111.7 na sayen na’urori masu kwakwalwa a wannan shekarar.
