Kakakin sojojin ?asar Manjo Ahmadou Abdrahamane ne ya sanar da juyin mulkin.
Sun sanar da rushe kundin tsarin mulkin ?asar, sannan kuma sun kulle duka iyakokin ?asar baki ?aya.
Babu dai labarin halin da Mohamed Bazoum ke ciki ya zuwa yanzu.
Amma sojojin sun bayar da sanarwar sun tu?e shi daga mu:?aminsa.
Sun ce sun yi juyin mulkin ne saboda halin da Nijar ke ciki na ta?ar?arewar tsaro da tattalin arzi?i.
Sun kuma sanar da dokar hana fita daga ?arfe 10 dare zuwa 6 na safe.
Shugaban ?asar Benin Patrice Talon wanda ke jagorantar tawagar ECOWAS na cikin ?asar, sai dai sun gaza cimma wata yarjejeniya da masu gadin shugaban ?asar da suka amshe mulkin.
Tun a safiyar jiya Laraba ne aka bayar da rahotannin tsare Shugaba Bazoum a gidan gwamnati, abin da ya janyo zanga-zanga daga magoya bayan Bazoum.
Sojoji sun yi harbe-harben jan kunne domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya nuna rashin goyon bayan wannan ?asarsa kan juyin mulkin.
Sakataren Majalisar ?inkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya yi magana da Shugaba Bazoum kuma ya tabbatar masa da cewa yana da goyon bayan Majalisar.
Wannan ne juyin mulki na hu?u da aka yi a Nijar tun bayan samun ‘yancin kai da ta yi daga Faransa a 1960, kuma an ta yin yunkurin junyin mulki da yawa a ?asar da ba su yi nasara ba.
