‘Yan sandan ?asar Jamus, a ranar Talata, sun bayyana cewa an sace kuros ?in da tsohon Fafaroma, Benedict XVI, ya saba sanyawa a ?irjinsa daga wata coci da ke kudancin ?asar. An ce Fafaroma Benedict ya sadaukar da kuros ?in da aka sace ga wata coci da ke mahaifarsa, wato Bavaria da ke ?asar Jamus, kamar yadda ABC News ta wallafa.
Barayin sun ha?a da satar ku?i baya ga kuros ?in Yan sandan sun bayyana cewa barayin da ba a san ko su waye ba, sun tafka mummunar satar ne a tsakanin ?arfe 11:45 na safe zuwa 05:00 na yammacin ranar Litinin.
Yan sandan sun kuma ce kuros ?in da aka ?auke, irin wanda ake ratayawa a wuya ne mai sauka akan ?irji. ‘Yan sanda na gudanar da bincike kan satar kuros ?in Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ce jami’an tsaro sun ?addamar da bincike kan satar, inda suke kiran mutane suna amsa tambayoyi dangane shige da ficen da mutane suka yi a kusa da cocin.
Bayanin ‘yan sandan ya ?ara da cewa, kuros ?in da aka sace wani abu ne mai matu?ar muhimmanci ga mabiya ?arikar katolika, inda suka nemi wa?anda suka ?auka su dawo da shi. A shekarar 2022 ne dai aka dawo da kuros ?in zuwa cocin da aka sace shi, bayan murabus daga shugabancin da Fafaroma Benedict XVI ?in ya yi, wanda kuma ya rasu a ?arshen shekarar.
