An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban kasar Senegal na biyar a tarihin kasar, a wani ?atsaitatcen biki da aka yi a wani ?akin taro da ke wajen birni Dakar.
Faye mai shekaru 44 sanye da baka?en kot, ya ?age hannunsa na dama, a gaban daruruwan jami’an kasar Senegal da kuma shugabannin kasashen Afirka bakwai da suka hallara zauren taro da ke cibiyar baje kolin sabon garin Diamniadio, wajen Dakar babban birinin kasar.
Diamaye Faye ya yi nasara da kashi 54 cikin dari na kuri’un da aka kada a za?en da aka jinkirta a kan abokin hamayyarsa na hadakar jam’iyya mai mulki.
A ranar Juma’a ne Kotun Kolin kasar ta yammacin Afirka, ta tabbatar da Mista Faye a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu wanda kuma shi ne shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO ya kasance cikin shugabanni kusan 15 ko wakilansu da suka halarci biki.
