Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa Wata kungiyar Arewa, Think Tank, ta bayyana cewa Arewa ba za ta iya dakatar da kudirin tazarcen Shugaban ?asa, Bola Ahmed Tinubu ba a babban za?en 2027.
A cewar ?ungiyar, a yanzu Arewa ba ta bukatar karfin siyasa, ta fi bu?atar shugaban da zai kula da shiyyar ta hanyar samar da ababuwan more rayuwa da ilimi.
Shugaban Arewa Think Tank, Muhammad Alhaji Yakubu, ne ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyin ?an jarida bayan taron addu’o’in ?arin shekara da suka shirya wa Tinibu a Kaduna.
Yakubu ya shawarci ‘yan Arewa su fada wa kansu gaskiya duk da tana da ?aci, su ajiye ra’ayin yanki a gefe, su marawa Tinubu baya a karo na biyu don a samu ci gaba a shiyyar.
