Wani dan majalisar tarayya daga jihar kebbi da ke Najeriya, Hon Kabir Ibrahim Tukura ya shaida wa Majalisar Wakilai cewar akalla mutane 500 ‘yan bindiga suka kashe a mazabar sa ta Sakaba da Danko Wasagu, yayin da akayi garkuwa da mutane 201 bayan raba mutane sama da 15,000 da muhallinsu,
Yayin da yake bayanin halin da jihar su ta samu kan ta sakamakon hare-haren ‘yan bindigar Tukura ya ce sabanin adadin mutane 88: da ‘yan sanda suka gabatar a matsayin wadanda aka kashe a makon jiya a kauyukan Koro da Kimi, da Gaya da Dimi da Zulu da Rafin Gora da D’lanko da Dguenge da Chonoko da Unashi a karamar hukumar Danko Wasagu, sun gano cewar adadin wadanda suka mutum ya zarce, 150,
Jaridar Daily Trust ta ruwaito dan majalisar na cewa bayan hallaka mutane an kuma sace shanu kusan 5,000: da tumaki 3,000: a cikin mako guda,
Dan Majalisar yace wa’dannan tarin ‘yan bindigar da ke dauke da muggan makamai na bi gari-gari, suna neman shanun da za su kwashe tar da kayan abinci da kuma satar mutane,
Tukura ya ce, ‘yan bindigar sun kuma kona wasu gidaje a kauyukan da suka kai hari abinda ya jefa rayuwar wadanda suka tsira daga hare-haren cikin tashin hankali,
Dan Majalisar ya ce, wa’dannan ‘yan bindiga basa barin mata ko yara yayin da suke kai irin wa’dannan hare-hare, wanda ke matukar illa ga jama’a da kuma yankunan su ganin yadda suke kashe su suke kuma yi musu fyade.
Tukura ya kara da cewa, lura da irin wannan kisa da kuma jikkata mutane, da ‘yan bindigar suka yi, ta tabbata cewar gwamnatin tarayya da ta jiha, ba su daukar matakan da suka dace domin kare rayukan jama’a, ganin yadda ‘yan bindigar suka mamaye wasu yankuna, suna iko da su wajen yin abinda suka ga dama.
