Kebbi: Ba Da Gaske Gwamna Yake A Yaki Da ‘Yan Bindiga Ba – Mafarauta

Rahotanni daga Jihar Kebbi na bayyana cewar Mafarauta da maharban da su ka fantsama daji domin ceto ?aliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri a Jihar sun ce sun daina neman yaran haka nan, domin gwamnatin jihar ba ta nuna masu cewa lallai da gaske ta ke yi, ta na so a sako yaran ba.

An dai kama ?aliban su 102 tun a ranar 17 Ga Maris. Sun shafe kwanaki 46 kenan a hannun ‘yan bindiga, duk da dai uku sun gudu, wasu uku kuma sun mutu wurin wani ?o?arin ku?utar da su da jami’an tsaro su ka yi.

Idan an tuna, Gwamna Abubakar Bagudu har tara mafarauta ya yi, ya ce ya amince zai shiga gaba ya ja zugar mafarauta domin a ceto ?aliban.

To sai dai kuma kwanaki 45 bayan yin garkuwa da yaran, Shugaban mafarautan mai suna Ardu Bagobiri, yace sun daina neman yaran, saboda a cewar sa, Gwamnatin Jihar Kebbi ta ?i tallafa masu da kayayyakin da za su yi amfani su shiga dajin da su, duk kuwa da cewa Gwamna Bagudu ya yi masu al?awarin haka.

“Mun nemi a ba mu makamai da babura, domin mu ri?a kutsawa cikin sur?u?in daji. Amma shiru ka ke ji har yau.

“Da farko an ba kowanen mu naira 30,000 aka ce ya bar wa iyalinsa kawai, shi kuma daga baya za a ba shi wani abu. Tun da aka ba mu Naira 5,000 har yau ba a sake ba mu ko sisi ba.”

“Ba fa haka mu ka yi gangami mu ka shiga daji ba. Gwamna ya tara mu, ya sa mana albarka, sannan ya ce zai taimaka mana. Amma shiru ka ke ji.

Sai dai kuma Kakakin Ya?a Labaran gwamnan Rabiu Kamba ya shaida wa manema labarai cewa Gwamna Bagudu bai manta da su ba. “Takardar neman kayayyakin shiga daji na a kan teburin gwamnan, jira kawai ake yi ya sa hannu.”

Related posts

Leave a Comment