Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Saudiyya ta kara wa’adin saukar jirage ga mahajjatan Najeriya daga 4 zuwa 6 ga watan Yuli
Daraktar kula da harkokin yada labarai ta hukumar Alhazzai Hajiya Fatima Usara ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar a Abuja.
Ta kara da cewa kara wa’adin ya zama wajibi ne sakamakon yawan jiragen da aka soke tashinsu da kuma wadanda aka samu jinkiri wajen tashinsu.
