?an bindigar da suka sace gami da yin garkuwa da ?aliban makarantar sakandaren Kimiyya ta maza da ke ?an?ara a Katsina, sun tuntu?i wasu daga cikin iyayen ?aliban, inda suka bu?aci a fara tara ku?a?en fansa.
A cewar Kadaria Ahmed, wata fitacciyar ‘yar jarida a Najeriya ta bayyana cewar Abdul Labaran, kakakin Gwamnatin jihar Katsina ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi da shi a RadioNow FM.
Ta ce ta jiyo labaran na cewa ?an bindigan sun fa?a wa iyaye su fara tanadin ku?in fansa kafin a sako ?aliban, kuma suyi komai cikin sirri ba tare da sanar da jami’an tsaro ba.
Kakakin Gwamnatin ya kuma ce ?an bindigan sun fa?a wa iyayen ?aliban su garga?i jami’an tsaro su daina musu ‘le?en asiri’ a inda suka ?oye idan ana son a samu ?aliban lafiya.
Kamar yadda Kadaria ta wallafa a shafinta na Twitter.
Amma a ?angaren ta helkwatar tsaro ta ce ba za a janye sojojin ba duk da maganar da ?an bindigan suka yi da gwamnatin jihar.
A hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Litinin, John Enenche, kakakin hedkwatar tsaro, ya ce ba za a dakatar da aikin ceto ?aliban da sojojin ke yi ba.
“Ba za a dakatar da aikin ceto da sojojin ke yi ba don wata tattaunawa. Ana iya dukkan biyun a lokaci guda,” in ji shi.
Ya ce idan aka kawar da kai daga inda ?aliban suke, za su sulale da su don haka ba za a yi sakaci ba don abinda ya fi muhimmanci a yanzu shine ceto ?aliban da lafiyarsu.
