Katsina Ta Dauki Saiti Karkashin Gwamna Dikko Radda – Lawal Kuraye

?an majalisar dokokin Katsina mai wakiltar karamar hukumar Charanci Honorabul Lawal Isah Kuraye ya bayyana cewar jihar Katsina a yanzu ta dauki saiti tun bayan kama ragamar jagorancin Gwamna Dikko Umar Radda.

?an majalisar ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawar da ya yi da wakilinmu a Kaduna dangane da salon mulki na sabon Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda.

Kuraye ya ?ara da cewar da akwai wasu tsare tsare da gwamnan ya fito dasu wa?anda za su taimaka matu?a wajen ciyar da jihar Katsina gaba da kuma Inganta rayuwar jama’ar jihar.

Dangane da matsalar tsaro dake addabar jihar Lawal Kuraye ya nuna gamsuwa da matakan da gwamna Dikko Radda ke dauka na maganin matsalar.
“Na san Dikko Umar Radda farin sani mun yi aiki tare yana shugaban ?aramar Hukumar Charanci ina mataimakin sa, mutum ne ?wararre mai himma wanda duk abin da ya sa a gaba sai ya yi maganin sa ina da yakinin Dikko Radda zai kai Katsina ga tudun mun tsira”.

Related posts

Leave a Comment