Hukumar Da?ile Cutuka Masu Ya?uwa ta Najeriya NCDC ta ce har yanzu cutar Anthrax – da wasu dabbobin ?asar ke fama da ita – ba ta ya?u zuwa ga bil-adama ba.
gidan Talbijin na ?asar NTA ya ambato shugaban hukumar, Dakta Nasir Ahmed na cewa hukumar na ci gaba da lura tare da sanya idanu, musamman a garin Suleja inda cutar ta fara ?ulla a ?asar.
Gwamnatin ?asar ?ar?ashin ma’aikatar lafiyar ?asar na ?arfafa gangamin wayar da kai kan alamomin cutar da yadda za a kauce wa ?aukar ta, musamman a masarautar Suleja da ke jihar Naija.
Sarkin Suleja Muhammadu Auwal Ibrahim ya yi kira da hakiman masarautar da su kai rahoton rashin lafiyar dabbobi a yankunansu, tare da kauce wa cin naman da likitocin dabbobi ba su tantace lafiyarsa ba.
Tuni dai gwamnatin ?asar ta bayyana sayen alluran riga-kafin cutar domin yi wa dabbobi a garin Suleja, inda cutar ta fara ?ulla.
Dabbobi na gida da na daji na kamuwa da cutar ne idan suka sha?e ta daga ?asa wadda ke ?unshe da ?wayoyin cutar ko kuma suka ci ciyawa ko shan ruwan da ke ?auke da ita.
Dabbobin da suka fi kamuwa da cutar sun ha?a da shanu da tumaki da awaki da kuma barewa.
Haka kuma likitoci sun ce mutane na kamuwa da cutar a lokacin da suka yi cu?anya da dabbobin da ke ?auke da cutar ko kuma suka ta?a wani abu da ya fito daga jikin dabbobin.
