Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya roki mazauna jihar su yafe masa duk wani kuskure da ya yi a zamanin mulkinsa na tsawon zango biyu dake gab da karewa, domin dace da samun rahamar Ubangiji.
Gwamna Masari ya nemi wannan afuwar ne a wurin taron ?addamar da kwamitin yakin neman za?en jam’iyyar APC a jihar ranar Litinin 31 ga watan Oktoba, 2022.
Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wurin kira ga mambobin APC, wa?anda ke ganin an musu ba dai-dai ba da su yafe musu, inda ya ?ara da cewa sun yafe wa kowa. Haka zalika, gwamnan ya maida martani ga wasu mutane da yake ganin sun yi wa jam’iyyar APC da gwamnatinsa butulci sakamakon rashin cika burin nasu.
“Akwai wasu da suka sami 80 cikin ?ari wasu kuma kaso 70 har da wa?anda 50 suka samu amma abin mamaki suka gaza gode wa Allah.”
Masari bai ambaci suna ba amma ana ganin daga cikin mutanen da yake nufi har da tsohon sakataren gwamnatinsa, Mustapha Inuwa. Dakta Inuwa ya sauya she?a zuwa jam’iyyar PDP bayan shan kaye a hannun Dikko Radda a za?en fidda ?an takarar gwamna a inuwar APC wanda ya gudana a watan Mayu.
