Katsina: An Damke Matar Da Ta Jefa Dan Kishiyarta A Rijiya

Rundunar ?an sanda a jihar Katsina ta kama Maryam Habibu, ?ar shekara 18 da haihuwa, bisa zarginta da jefa ?an kishiyarta mai shekaru hudu cikin rijiya a ?aramar hukumar ?afur ta jihar.

Maryam wadda ta fito daga ?auyen Leko da ke ?aramar hukumar ?anja tare da wasu mutane 11 da ake tuhuma da laifuka daban-daban da suka ha?a da fashi da makami da satar shanu, an gabatar dasu a ranar Juma’a a shelkwatar ?an sanda da ke Katsina.

Kakakin rundunar ?an sandan, SP Gambo Isah, yayin da yake zantawa da manema labarai yayin holan, ya bayyana cewa an kama matar ne a ranar 9 ga Nuwambar 2022. Ya ci gaba da bayyana cewar ta fitar da yaron ne ta jefa shi cikin rijiya. Kakakin ya ce Maryam da mahaifin yaron sun rabu.

Manema labarai sun rawaito cewa Maryam wadda ta zanta da manema labaran cikin harshen Hausa, ta amince da aikata laifin, tana mai cewa ?addara ce a wasa abun ya faru.

A cewarta, “Gaskiya ne na jefa yaron a cikin rijiyar da ya mutu amma Allah ne ya yi zai mutu a ranar. Shi ya sa ya rasu.”

Related posts

Leave a Comment