2023: INEC Ta Haramta Yakin Neman Zabe A Masallatai Da Coci-Coci

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da babban za?e na 2023 ke ?aratowa a Najeriya, hukumar za?e ta ?asa mai zaman kanta (INEC) ta hana ‘yan siyasa ya?in neman za?e a masallatai da coci-coci.

Hanin na cikin kundin ?a’idojin kamfe da hukumar INEC ta fitar a ranar Alhamis game da yadda jam’iyyu da ‘yan siyasa za su gudanar da ya?in neman za?uka da kuma adadin ku?in da za su iya kashewa.

“Kar a yi ya?in neman za?e a wuraren ibada, da ofisoshin ‘yan sanda da kuma ofisoshin gwamnati,” a cewar INEC.

Kazalika, kundin ya ce “kar a yi amfani da kalaman ?atanci ko kuma kalaman ?iyayya yayin ya?in neman za?e”.

Bugu da ?ari, “kar wani mutum ya ?auki makami zuwa wurin taron kamfe ko kuma maci”.

Related posts

Leave a Comment