Karin Kwanaki 10 Na Daina Karbar Tsoffin Kudi Ya Yi Kadan – Majalisa

Kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan sauya fasali da musanya tsoffin ku?i ya yi fatali da ?arin wa’adin kwana 10 da Babban Bankin ?asar ya yi na amfani da tsoffin takardun ku?i.

A wata sanarwa da gwamnan Babban Bankin Godwin Emefiele ya fitar ranar Lahadi ya ce shugaban ?asar Muhammdu Buhari ne ya sahale wa CBN ?in yin ?arin wa’adin zuwa ranar 10 ga watan fabrairu.

To sai dai a martanin kwamitin ?ar?ashin jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Ado Doguwa, ya yi watsi da ?arain wa’adin, yana mai cewa dole CBN ya yi biyayya da sashe na 20, ?aramin kashi na 3, da 4 da kuma 5 na dokar CBN.

Idan za a iya tunawa dai a ranar Talata ne majalisar ta kafa kwamitin da zai duba batun wa’adin da CBN ?in ya saka, bayan ‘yan ?asar da dama sun yi ta kokawa kan irin wahalhalun da suke sha a ?o?arinsu na musanya ku?adensu.

Doguwa ya ce “Wa’adin kwana 10 da CBN din ya ?ara ba mafita ba ne, mu abin da kawai muke bu?ata a matsayinmu na ‘yan majalisa shi ne CBN ya yi biyayya ga sashe na 20 ?aramin kashi na 3 da na 4 da kuma na 5 na dokar CBN”.

” A matsayin Najeriya na ?asa mai tasowa, kuma mai bin tafarkin dimokradiyya dole mu yi biyayya da abinda doka ta tanadar.

Ya ?ara da cewa majalisar wakilan za ta bayar da umarnin kamo gwamnan Babban Bankin domin tilasta masa bayyana a gaban kwamitin.

Doguwa ya ci gaba da cewa kwamitinsa zai ci gaba da aiki har sai ya tabbatar da biyan bu?atun ‘yan ?asar kamar yadda doka ta tanadar.

Yayin da yake bayyana ?arin wa’adin kwana 10 da cewa ba wani abu ba ne illa yaudarar ‘yan ?asar tare da ?ara jefa tattalin arzikin ?asar cikin halin ni-‘yasu, Doguwa ya ce dole ne gwamnan Babban Bankin ya bayyana a gaban Majalisar wakilan ko kuma ya fuskancoi barazanar kama shi, ta hanyar yin amfani da ?arfin da doka ta bai wa majalisar.

Doguwa ya kuma ce matakin na Babban Banki na iya yin barazana ga babban za?en da ke tafe.

Related posts

Leave a Comment