Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da ?ara wa’adin daina kar?ar tsofaffin takardun ku?i zuwa 10 ga watan Fabirairu.
Gwamnan Babban Bankin Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Gwamnan ya ce ya zuwa yanzu CBN ya kar?i naira tiriliyan ?aya da biliyan 900 na tsoffin takardun ku?i, inda kuma ya ce saura naira biliyan 900 ya kammala kar?ar tsoffin takardun ku?a?en.
Ya yi bayanin cewa sai da CBN ya nemi sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari domin ?age wa’adin kar?ar tsofaffin takardun ku?in, wanda kuma ya amince a ?ara wa’adin da kwana 10.
“Sakamakon halin da ake ciki, mun nemi umarni kuma mun samu daga shugaban ?asa kamar haka: ?arin kwanki 10 na kar?ar tsofaffin takardun ku?i daga 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan gobe na Fabrairu, za a ci gaba da kar?ar ku?in daga hannun ‘yan Najeriya a hukumance,” in ji sanarwar.
“Dama ta kwana bakwai, daga 10 zuwa 17 ga watan Fabrairu, domin al’umma su iya mayar da tsoffin ku?adensu Babban Bankin Najeriya bayan cikar wa’adi, kamar yadda doka ta 20(3) da ta 22 ta Babban Bankin ta tanada”.
“Bayanan da muka samu tun daga 2015, sun nuna ku?a?en da ke yawo a hannun ‘yan Najeriya sun kai naira tiriliyan ?aya da biliyan 400. Amma ya zuwa watan Oktoban 2022, al?aluma sun nuna cewa akwai sama da tiriliyan uku da biliyan 230 da ke yawo a hannu mutane.
“Wannan na nuna cewa naira biliyan 500 ne kacal a hannun bankuna, yayin da naira tiriliyan biyu da biliyan 700 ke ?oye a hannun wasu ?alilan.”
Gwamnan CBN ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zama masu biyayya da ha?in kai wajen tabbatar an gama mayar da ku?a?en ba tare da wani tashin hankali ba.
Gabanin wannan mataki dai, da dama daga cikin ‘yan Najeriya sun fuskanci yanayi maras da?i wajen mayar da tsofaffin ku?a?ensu zuwa bankuna.
Cikin sanarwar gwamnan Babban Bankin ya yaba wa Shugaba Buhari na ha?in kai da ya bai wa CBN domin gabatar da wannan sauyin ku?in wanda ya ce “ya kamata a ri?a yi duk shekara biyar zuwa takwas, amma Najeriya yanzu ta shafe shekara 19 ba ta sauya nata ku?a?en ba”.
Manyan ‘yan siyasa a Najeriya irin su Atiku Abubakar da Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi da Bola Ahmed Tinubu sun yi kira ga CBN ?in da ya ?ara wa’adin kar?ar tsoffin takardun ku?in.
