Karin Kudin Aikin Hajji: Dubban Maniyyata Za Su Hakura Da Sauke Farali A Bana

images 2024 03 26T080553.731

Yayin da Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ?ara ku?in kujerar aikin Hajjin bana da miliyan ?aya da dubu ?ari tara, ana fargabar cewa da wuya maniyyatan bana su iya cikawa.

A ranar Lahadi ne hukumar alhazan ta sanar da ?arin tana cewa hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala, wadda da ita ce ake yin ?iyasin dukkanin abubuwan da maniyyata ke bu?ata a Saudiyya.

Wannan ne karo na biyu da hukumar alhazan ke ?ara ku?in kujera a bana, abin da ya sa ake ganin da wuya a gudanar da aikin Hajjin da wasu maniyyatan Najeriya, wadanda suka jima da fara ajiye ?udin kujerar.

Kazalika, wasu na ganin wa’adin cika ?udin da hukumar alhazan ta bayar na kwana hu?u na cikin abubuwan da za su sa maniyyatan na bana su ha?ura da zuwa aikin Hajjin.

Wani maniyyaci a Abuja babban birnin Najeriya da BBC ta tuntu?a ya ce ya yanke shawarar bin kiraye-kirayen da malamai suka yi na ciyar da al’umma da ku?in Hajjin nasa.

“Duba da yanayin da ake ciki a yanzu na tsadar rayuwa, gara mu ciyar da marasa ?arfi,” in ji shi.

Related posts

Leave a Comment