Kotun koli ta tabbatar da cin gashin kan kananan hukumomi 774 na Najeriya, ku?a?en su su shiga aljihun su darek ba tare da gwamnoni sun yi musu katsalandan ba.
A hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis, kwamitin mutane bakwai na kotun ya amince da kararrakin da gwamnatin tarayya ta gabatar na karfafa ‘yancin kananan hukumomin kasar nan.
?aya daga cikin mambobin kwamitin, Emmanuel Agim, wanda ya gabatar da hukuncin kotun, ya ce daga ranar Alhamis ya kamata kananan hukumomin kasar nan su karbi kason su kai tsaye daga hannun Akanta Janar na Tarayya.
Sabon tsarin da Kotun Koli ta bayar ya baiwa Akanta-Janar na Tarayya damar ketare gwamnatocin Jihohi wajen rabon kudaden da gwamnatin tarayya ke rabawa kananan hukumomi duk wata wanda a baya sai ya bi ta hannun gwamnatocin jihohi tukunna.
Shekaru 20 kenan kananan hukumomi na yin bauta ga jihohi, sun zame bayin jihohi, sai abinda aka ba su, wanda ba ya wuce su iya biyan albashi kawai.
Gwamnoni ke za?en wanda suke so su kuma tsige wanda suke so. Babu aikin da karamar hukuma za ta iya yi sai abin da gwamnoni suka ce shi za a yi.
Bisa ga hukuncin kotun koli, daga wannan wata ta Yuli, kowacce karamar hukuma za ta rika amsar ku?in ta kai tsaye ne daga asusun gwamnatin tarayya, ba tare da wani gwamna ya yi mata tsalandan ba.
A baya akan samu ayyukan cigaba matuka karkashin kananan hukumomi, amma tun bayan sauya fasalin samun kudaden su lamarin ya canja. Iya ka su je aiki, idan wata ya ?are su kar?i albashi kowa ya kama gaban shi.
