Kano: Talauci Ya Sa Jama’a Cin Bashin Garin Tuwo

Labarin dake shigo mana daga birnin Kano jalla babbar Hausa na bayyana cewa duk da cewa tashin farashin kayayyaki a Najeriya bai kai ?ololuwa ba amma talakawa na matu?ar shan wahala a sakamakon haka.

BBC ta yi wani bincike game da yadda mutane da yawa ke gudanar da rayuwarsu a ?asar da matsin tattalin arzi?in ta ke neman yi wa katutu.

Najeriya wadda ita ce ?asa mafi girman tattalin arzi?i a Afrika na fuskantar tsadar rayuwa tun gabanin shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai a watan Mayu, abin da ya ?ara ta’azzara yanayin.

Ga wata matashiya ‘yar shekara 18 da ke zaune a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, kullum da safe tana zagayawa gidaje daban-daban domin ro?o abin da za su karin kumallo da shi.

Sama da shekara guda ita da ‘yar uwatta ce ke samar da abincin da ake ci a gidansu da ake da yara shida, safe da rana da kuma dare.

fg

“Ba haka rayuwarmu take ba a baya, wa?annan sauye-sauyen da aka samu ne suka shafe mu.

“Mahaifunmu sayar da kaya yake a kasuwar kwari gabanin abubuwa su ta?ar?are masa ya zama ko abinci bai iya saya mana.”

Ta ce duka gidansu babu mai zuwa makaranta, babban abin da yake gabansu a yanzu shi ne yadda za su tsira daga yunwa.

Gidaje da dama a Najeriya na cikin irin wannan yanayi da gidansu matashiyar nan ke ciki, kuma mutane da yawa wannan labarin nata ba zai ba su mamaki ba saboda sabo da suka yi da yanayin da ake ciki.

Wani mutumi kuma ya fito a gidan wani radiyo a Kano, ya bayar da labarin yadda mutane ke karbar bashin garin tuwo domin dafawa a ci.

Kwanakin da suka gabata ne ?ungiyar masu biredi a ?asar ta ce ta yi ?arin kashi 15 cikin 100 na farashin biredin.

A cewar al?aluman baya-bayan nan, an samu ?arin farashin kayayyaki zuwa 22.79 daga 22.41 a watan Mayu, wannan ne wata na hu?u a jere da ake samun tashin farashin.

Hauhawar farashin ta fi shafar farashin abinci da hayar gida da ruwa da wuta da kuma man fetur.

Related posts

Leave a Comment