Bayan kira daga ?angarori da dama ga Gwamnatin Jahar Kano akan ta taka burki ga sana’ar bara barkatai akan titi, Gwamnatin Jahar ta shirya kafa hukumar hana bara akan titi tare da hadin gwuiwa da kungiyoyin fararen hula.
Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka a lokacin da yake kar?ar ba?uncin shuwagabancin ha?a??iyar ?ungiyar fararen hula ta jahar, a wata ziyara a lokacin taron Majalisar Zartaswa ta jahar, a ranar Talata a gidan Gwamnatin Jahar.
Tawagar ta samu jagorancin Malam Ibrahim Waiya, wanda ya jagoranci sauran shuwagabannin ?ungiyoyin daban-daban, domin su ?ara yin kira akan yawon barace-barace akan titi.Gwamnan Kano Umar Abdullahi Ganduje
Wannan na ?unshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren ya?a labarai na Gwamnan Abba Anwar ya fitar, a ranar 26 ga watan Satumba na Shekarar 2021.
Gwamna Ganduje yace “za’a samar da hukuma da ma’aikata da zasu duba al’amarin bara akan titi. Domin bazamu iya rike hannun mu ba, muga rayuwar ?ananan yara da basu san komai ba, an ?ata ta, ta hanyar wannan matsalar barace-barace.
Ya jaddada cewa, yawon barace-barace cin zarafin ?ananan yara ne, wanda ya bayyana a matsayin abinda yake hana yaran karatun addini da ilmin zamani.
A lokacin da yake yabawa da irin damuwa da ?ungiyoyin fararen hular suka nuna, ya bada tabbacin cewa, gwamnatin jahar zata tafi da kowa da kowa, domin samun nasarar gudanar da wannan tsari na hana yawon barace-barace akan titi.
“Muna farin cikin ?arbar ku, kuma muna godiya da damuwa da kuke yawan nuna wa. Gaskiyane cewa, dole mu samo wasu dabaru da za’ayi amfani dasu wajen kula da matsalar,” inji shi.
Tunda Farko, ha?a??iyar ?ungiyar fararen hular sun turowa gwamnan takarda, inda suke bu?atar da a ha?a hannu dasu domin samun nasarar kafa doka akan hana yawon barace-barace.
An turo takardar a ?ar?ashin inuwar ha?a??iyar ?ungiyar fararen hular mai kwanan wata 23 ga watan Satumba na shekarar 2021, mai taken “kira na gaggawa akan dokar hana bara a jahar Kano
tare da sa hannun Ibrahim Waiya da Peter Hassan Tijjani
A matsayina na Gwamna ina mai tabbatar maku da cewa takarda
tayi dai-dai da abinda ke cikin zuciyar mu akan hakan.
