?ungiyar Dattawan Arewan Nigeria a ranar Talata, ta yabawa Gwamnonin yankin Arewa, da suka ?i amincewa da tsarin karba-karba na shugaban ?asa ya zuwa yankin kudu, kamar yadda Kungiyar Gwamnonin Kudu ke nuna bu?atar hakan.
Mai Magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewar Baba-Ahmed ya bayyana haka, a lokacin da yake jawabi ga taron manema labaru Kaduna a ranar Talata, inda ya bayyana bu?atar Gwamnonin Kudu na amsar shuwagabancin ?asar a shekarar 2023 a matsayin abinda ba za’a ta?a yarda ba.
A cewar sa, duk wani shugaba da za’a za?a, dole ayi hakan ta hanyar dimokura?iyya, ba ta hanyar barazana da nuna fin ?arfi.
Yace “munyi wannan maganar a makonni biyu da suka gabata, muna farin ciki ganin yadda Gwamnonin kudu sun yi magana akan hakan. Tsarin kar?a-kar?a baya cikin kundin tsarin mulkin ?asar, amma wannan bai sanya ya zama ba halattacce ba, ko kuma a matakin siyasa ka?ai za’a iya hakan.
“Muna janyo hankali akan cewa, akwai yiwuwar Gwamnoni 17 na kudu su ha?a kawunan su, domin cin mutuncin ?an arewa, ta hanyar sanya dokar hana kiwo a fili, tsarin kar?a-kar?a na shugaban ?asa da sauran al’amurra.
“Gwamnonin kudu suke kawo tsaiko a tsarin dimokura?iyya. Abinda dimokura?iyya ta yarda dashi shine akwai jami’iyyun siyasa, akwai ?an takara, akwai kuma masu ka?a kuri’a, duk wanda yaci zabe, sai ya zama ?an takara, wanda daganan sai ayi sasanci.”
Baba-Ahmed yace Dattawan Arewa nason ?an Nigeria dasu fahimci cewa har yanzu ana mutunta dimokura?iyya, a saboda haka bazasu, bazasu iya nuna yadda shugabancin ?asa zai kasance.
