Kano: Ruwa Ya Ci Rayukan Wasu Aminai Uku


Ranar Laraba, 18 ga watan Mayun 2022, rana ce da jama’ar garin Bichi a Jihar Kano ba za su ta?a mantawa da ita ba, musamman Idris Umar wanda yana tsaye mutum uku daga cikin abokansa suka rasu bayan sun nutse a cikin ruwa a ?araye a lokacin da suka je wanka a Kogi da safe.

Musa Abubakar mai shekara 25 da Isyaku Bashir, mai shekara 23 da kuma Nazifi Ibrahim mai shekara 19, duk sun rasu a lokacin da suka shiga dam don su yi wanka da misalin ?arfe 11:00 na safe.

Idris ya shaida wa BBC cewa shi da sauran abokansa sun yi tafiya daga Bichi zuwa ?araye a ranar Talata domin zaman Majalisi.

“Wasu mutane ne a Karaye suka neme mu domin zuwa Majalisin kuma ya kamata mu koma Bichi a ranar amma sai suka ro?e mu da mu ?ara wasu sa’o’i, ko da yamma ta yi sai suka ce mu kwana a Karaye, in ji Idris.

“Da safe, sai aka rin?a jinkiri wurin kawo ruwan wanka sai ?aya daga cikinmu ya ba mu shawarar mu je kogi mu yi wanka wanda daga nan ne muka soma tafiya.

“Wasu daga cikinmu ba su saki jiki da dam ?in ba inda suka ce kada mu je saboda wani mummunan abu zai iya faruwa amma sai Musa (yana cikin wa?anda suka rasu) sai cikin wasa ya ce babu abin da zai faru.”

Sai Idris ya ci gaba da bayani kan abin da ya faru a lokacin da suka kai dam ?in da kuma yadda abokansa uku suka rasu cikin mintoci.

“Dam ?in yana da ?angarori biyu, akwai babban wurin wanda muka ?aurace masa sa’annan akwai ?aramin wurin wanda can muka je kuma har muka ga ?ananan yara a wurin da ke wanka.

“Isyaku ne ya soma cire kayansa ya tsunduma cikin ruwan sa’annan Nazifi ya bi shi amma hu?u daga cikinmu sai muka lura cewa ba su fito ba, wanda hakan ya sa Musa ya ce bari ya shiga ya ceto su.

“Ko da Musa ya shiga sai muka lura cewa wani mummunan abu ya faru saboda babu wanda ya fito daga cikinsu sai muka soma ihun kiran mutane.

“Amma abin takaicin shi ne ba a kawo ?auki da wuri ba saboda bayan minti goma da kusan mutum 20 suka shiga nemansu gawarwakinsu ka?ai aka ciro daga dam ?in.”

Idris ya ce shi da sauran abokansa ba su iya ruwa ba shi yasa suka yanke hukuncin cewa ba za su shiga neman abokansu ba.

Mahaifin Musa ya bayyana cewa ba zai manta lokacinsu na ?arshe tare da ?ansa ba kafin suka kama hanyar zuwa Karaye.

“Ina kwance a ?aki a lokacin da Musa ya shigo ya gaishe ni ?auke da jaka inda ya ce mani Baba za mu tafi Karaye domin yabon Annabi ni kuma sai na yi masa addu’ar Allah ya tsare su.”

Mahaifin ya bayyana cewa ba iyalansa ka?ai za su yi kewar Musa ba, a fa?in Bichi ana amfana da shi sakamakon yana da shaguna biyu na POS wanda yake taimakawa domin cire ku?i.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana reshen Jihar Kano Saminu Yusuf ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce ba a tuntu?e su ba wurin neman ?auki kuma a lokacin da suka isa wurin masu iyo a cikin ruwa tuni suka ciro gawarwakinsu daga dam ?in.

Ya bayar da shawara ga musamman ba?i da su guji shiga ruwan da ba su saba da shi ba.

Related posts

Leave a Comment