Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar jam’iyyar NNPP ta sake yin kamu a jihar inda ta samu karin mabiya a makon nan.
Jam’iyyar hamayyar ta NNPP ta samu karin ‘yan majalisar dokoki uku da suka sauya-sheka daga APC kamar yadda suka sanar a wasikar da suka fitar.
A mabanbantan takardu da suka aikawa shugaban majalisar Kano a ranar 5 ga watan Mayun 2022, sun sanar da ficewa daga APC da kuma komawarsu sabuwar jam’iyyar NNPP.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na majalisar dokokin jihar Kano, Uba Abdullahi ya kawo sunayen wadanda suka fice daga jam’iyyar mai mulki ta APC zuwa sabuwar jam’iyyar NNPP.
Akwai Hon Abdullahi Iliyasu Yaryasa mai wakiltar mazabar Tudun Wada. Sai kuma Hon. Muhd Bello Butu Butu mai wakiltar mutanen Tofa da Rimin Gado, na uku a jerin shi ne Hon. Kabiru Yusuf Ismail, ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Madobi.
Hakan na nufin an samu masu sauya-shekan daga kowane yanki na Kano. Yayarsa ya fito ne daga kudancin jihar, Butu Butu kuma yana Arewacin jihar Kano. Kabiru Yusuf Ismail shi ne yake daga garin Madobi a shiyyar Kano ta tsakiya.
Malam Uba Abdullahi ya ce majalisa ta yi wadanda suka fice daga jam’iyyar APC fatan alheri.
