Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana ya?inin da yake dashi na samun nasarar Tinubu a babban zaben dake tafe na shekarar 2023:
Babachir ya bayyana haka ne a Abuja, a ranar Laraba, 11 ga watan Afrilu, jim kadan bayan wata kungiyar goyon bayan Tinubu ta mika fom din takarar shugaban kasa na Tinubu a sakatariyar jam’iyar APC na Kasa.
Tawagar magoya bayan Tinubu karkashin jagorancin gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da Hon. James Abiodun Faleke ne suka mika fom din.
Kungiyar magoya bayan Tinubu ta TSG ce ta siya masa fom din takarar domin shiga takarar shugabancin kasa na APC wanda za a yi a ranar 30 ga watan Mayu.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan mika fom din, tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya ce koda dai Tinubu na cikin takarar don nasara ne, shi dan damokradiyya ne kuma ba zai tayar da tarzoma ba idan ya sha kaye.
“Mun ji dadi cewa a yau mun zo mika fom din nasara kuma mun cika daya daga cikin manyan bukatun jam’iyyar na tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC. Mun yi duk abin da ake bukata mun gabatar da duk takardun da ake bukata.
“Kamar yadda kuke gani, mun sami kwafin takardar amincewar mu kuma muna da tabbacin nasara zai zama namu a ranar 30 ga watan Mayu a yayin babban taron”.
