Za A Kashe Miliyoyi Domin Bunkasa Ilimi A Jihar Kano- Ganduje

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewa Hukumar FCDO mai kula da cigaban kasasshen renon Afrika ta na hasashen kashe Euro miliyan 14.7 a jihar Kano domin bun?asa harkar ilimi.

Birtaniya ta ce za ta batar da fam miliyan 14 a kan mutanen Kano domin bunkasa ilimi da sauran bangarorin cigaban al’umma. Rahoton da aka fitar a ranar 12 ga watan Agusta, 2021, ya ce babban jami’in FCDO, Dr. Chris Pycroft, ya bayyana haka da ya kai ziyara zuwa Kano a ranar Laraba.

Dr. Christopher Pycroft ya yi wani zama na musamman da gwamnatin Abdullahi Ganduje a karkashin yarjejeniyar MAD a gidan gwamnatin Kano. Christopher Pycroft, shi ne babban darektan da ke kula da cigaban ayyukan FCDO a Najeriya.

Gwamnatin kasar Ingila ta zaftare 29% daga cikin kasafin kudin abin da ta ke tallafa wa kasashen da ta rena, hakan ya sa tallafin ya ragu daga 0.7% zuwa 0.5%. Darektan na FCDO yace a wannan karo za a maida hankali ne wajen ayyukan cigaba da inganta rayuwar marasa galihu a jihohin Kano, Kaduna da Jigawa.

A maimakon bada gudumuwar tsabar kudi da marasa karfi, FCDO za ta taimaka wajen rage talauci ta hanyar bunkasa sha’anin kiwon lafiya, ilmi da sauransu. A shekaru bakwai da suka wuce tsakanin 2014 da 2021, FCDO ta kashe fam miliyan £130 a jihar Kano. Daga shekarar bara zuwa bana, hukumar ta kashe £14.7.

Related posts

Leave a Comment