Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mi?a mulkin Kano hannun mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna kamar yadda doka ta tanada yayin da Gwamnan ya bar jihar.
Ganduje ya yi haka ne jim ka?am kafin ?agawar Jirginsa zuwa ha?a??iyar daular larabawa (UAE) ranar Laraba a Abuja.
Kwamishinan ya?a labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Ya ce gwamna Ganduje zai halarci taron zuba hannun jari da kungiyar gwamnonin Najeriya NGF ta shige gaba a ?asar Larabawa, bisa haka Gawuna zai zama mu?addashin gwamna.
Sanarwan ta kuma umarci kwamishinoni, shugabannin ma’aikatu, daraktoci da sauran ?usoshin gwamnati da sauransu, su ba mu?addashin gwamna goyon baya da ha?in kai.
Haka nan kuma sanarwar ta yi bayanin cewa duk wani lamari da ake bukatar sa hannun gwamna a mi?a shi ofishin mataimakin gwamna.
Rahoto ya nuna cewa Ganduje ya jima ba shi a Kano na tsawon lokaci, kuma ya taka muhimmiyar rawa a gangamin APC na ?asa da aka kammala kwanan nan.
Ko a wannan makon, taron majalisar zartarwa na gwamnatin jihar Kano ya gudana ne a gidan gwamna dake Asokoro, babban birnin tarayya Abuja. Bayan kammala taron ne gwamnan ya kama hanyar zuwa hadaddiyar daular Larabawa UAE bayan mi?a ragamar komai hannun Nasiru Gawuna.
