Abdullahi Adamu Ya Karbi Ragamar Shugabancin APC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sabon shugaban jam’iyyar APC ta ?asa, Sanata Abdullahi Adamu, ya karbi jagorancin jam’iyya ta ?asa daga hannun shugaban riko Mai Mala Buni.

Wannan na ?unshe ne a wata sanarwa da jam’iyya mai mulkin ?asar nan APC ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta Twitter.

Hakan ya kawo ?arshen tsawon watanni 21 da Buni ya jagoranci APC tun bayan na?a shi shugaban kwamitin riko bayan saukar tsohon shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole.

Taron mi?a ragamar jagorancin jam’iyya ya gudana ne a babban ?akin taro na kwamitin NWC dake Sakatariyar APC ta ?asa a babban birnin tarayya Abuja.

Sabon shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya karbi kayayyakin ofishinsa daga hannun shugaba mai barin gado kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a Sakatariyar jam’iyya dake Abuja.

Sanata Adamu ya fitar da jawabi a shafinsa na dandalin Twitter yayin da ya tura Hotunan taron mi?a masa ragamar mulkin APC. Ya ce: “A wurin kar?an ragama a hukumance yau, shugaba mai barin gado, Mala Buni ya mana fatan Alkairi. Mun yi wa mutane al?awari cewa da zaran mun fara aiki jam’iyyar mu zata shiga mataki na gaba.”

Related posts

Leave a Comment