Kano: An Shiga Rudani Bayan Mutuwar Dalibar Jami’ar Bayero

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Wata daliba dake ajin ?arshe a tsangayar Ilimi ta jami’ar Bayero dake Kano (BUK), Binta Isa, ta rasu a ?akin kwanan dalibai ranar Juma’a 26 ga watan Nuwamba, 2021.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’ar ta fitar a shafinta na Facebook ?auke da sa hannun mataimakin rijistara, Lamara Garba.

?alibar wacce ta fito daga jihar Kogi, ta rasa rayuwarta ne da misalin ?arfe 7:00 na dare bayan fama da gajeruwar rashin lafiya da ta danganci ciwan ?irji.

A cewar daraktan lafiya na jami’ar, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, Binta ta je Asibitin jami’a na New Campus a ranar 24 ga watan Nuwamba, inda ta yi korafin tana fama da ciwan ?irji.

Ya ?ara da cewa jami’an da suka duba mamaciyar a lokacin, sun bata magani tare da zayyana mata yadda zata yi amfani da su. Daraktan ya bayyana cewa daga nan Binta ta samu sauki, domin ta cigaba da halartan Lakca ranar Alhamis da Jumu’a, kuma ta cigaba da ayyukan karatunta.

“A ranar Jumu’a 26 ga watan Nuwamba, 2021 da yamma, lokacin sallar Magriba, ta shaida wa abokiyar zaman ?akinta cewa tana jin ciwan ?irji, amma a haka ta kokarta ta yi Alwala domin ta yi sallar Magrib a ?akin.”

“Abokan zamanta a ?akin sun ka?u kuma sun tsorata da suka dawo suka tarad da ita ta yi warwas a ?asa.” “Nan take suka sanar da mutane, akai gaggawar kaita asibitin koyarwa na Aminu Kano, inda likita ya tabbatar da cewa ta rasu.”

Mataimakin shugaban BUK, Farfesa Sagir Adamu Abbas, tare da rijistara, Jamil Ahmad Salim, daraktan lafiya da darakan tsaro, Abdulyakin Ibrahim duk sun halarci wurin da lamarin ya faru.

A halin yanzun jami’a ta sanar da ?an uwan ?alibar, wanda yake zaune a cikin garin Kano, game da lamarin da ya faru BUK ta yi jimamin wannan rashi VC Farfesa Adamu, a madadin jagororin BUK, malamai da ?alibai, ya bayyana damuwarsa da rasuwar matashiya Binta Isa, wacce ta mutu ta na gab da kammala karatunta.

Ya kuma mika ta’aziyya ga iyayenta, yan uwa da abokan karatu, kuma ya yi addu’a Allah ya yafe mata kura-kuranta, ya sa tana daga cikin yan Aljanna.

Related posts

Leave a Comment