Kano: An Jirkita Kalaman AbdulJabbar Ne – Iyalan Nasiru Kabara

Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar ‘Ya ‘ya 18 daga gidan darikar Qadiriyya watau Sheikh Nasiru Kabara, sun rubuta takarda ta musamman zuwa ga fadar shugaban kasar Najeriya.

Wadannan mutane sun bukaci gwamnatin tarayya ta tsoma bakin ta a cikin abin da su ka kira muzguna wa ‘danuwansu, Abduljabbar Nasiru Kabara.

An ruwaito cewa wannan wasika da ta fito daga gidan na Qadiriyya a jihar Kano. A wannan takarda, ‘yanuwan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sun wanke shehin daga zargin da ake yi masa, suka ce an jirkita karatun da ya gabatar.

Wadannan shehunnai; maza da mata sun shaida wa shugaban kasa cewa an bankara karatun Abduljabbar Kabara ne domin a kama shi da laifin batanci.

Abin da wasikar ta kunsa “Tare da girmama wa da kan-kan da kai gare ka ran ka ya dade, mu ‘ya ‘ya (maza da mata) na Maulana Sheikh (Dr.) Muhammad Nasiru Kabara, mu na bukatar mu kawo kuka a gabanka, a matsayinka na shugaba kuma uban kowa, wanda ba zai taba goyon bayan rashin adalci ba.”

“Muna amfani da wannan dama domin kawo korafi game da ‘danuwan mu na jini, Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara, wanda wasu malaman Kano suka taso a gaba saboda sabani na gaira babu dalili, da yake tsakaninsu.”

“Wannan sabani ya jawo suka rika murguda karatuttukan ‘danuwanmu da aka dauka, domin su yi masa sharrin cin zarafin Annabi Muhammad (SAW), da nufin a kassara shi gaba daya.”

“Muna tabbatar maka cewa duk zargin da wadannan ‘malamai’ suke yi a kan ‘danuwanmu, kage ne, da gangan aka kirkiro su saboda manufa.”

Shehunan suka ce abin da ake kokarin laka wa ‘danuwansu, shi ne abin da yake ta yaki da shi.

Wadanda suka sa hannu a takardar daga ciki akwai maza biyar, da kuma mata 13.

1. Sheikh Ibrahim Mu’azzam Sheikh Nasir Kabara 2. Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Sheikh Nasir Kabara 3. Malam Askiya Sheikh Nasir Kabara 4. Malam Yahya Sheikh Nasir Kabara 5. Malam Aburumana Sheikh Nasir Kabara 6. Sayyidah Saratu Sheikh Nasir Kabara 7. Sayyidah Nafisatu Sheikh Nasir Kabara 8. Sayyidah Khudriyyah Sheikh Nasir Kabara 9. Sayyidah Zam’atu Sheikh Nasir Kabara 10. Sayyidah Saffanatu Sheikh Nasir Kabara 11. Sayyidah Aishatu Mannubiyyah Sheikh Nasir Kabara 12. Sayyidah Ummu Aimanal Habashiyyah Sheikh Nasir Kabara 13. Sayyidah Khadijatul Habashiyyah Sheikh Nasir Kabara (II) 14. Sayyidah Huza’iyyah Sheikh Nasir Kabara 15. Sayyidah Jamila Sheikh Nasir Kabara 16. Sayyidah Bulkisu Sheikh Nasir Kabara 17. Sayyidah Rukayya Sheikh Nasir Kabara 18. Sayyidah Hansa’u Sheikh Nasir Kabara.

Yanuwan malamin sun kira kansu da UNITED FORUM OF SHEIKH NASIR KABARA’S DESCENDANTS, ma’ana kungiyar hadin-kan tatson Nasiru Kabara. Jagoran gidan a nan shi ne Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Nasiru Kabara.

Related posts

Leave a Comment