Kano: An Haramta Yin Finafinan Masu Garkuwa Da Mutane

Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin jihar ?arkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta hana yin fim ?in satar mutane da na shan ?waya.

Hakazalika Gwamnatin jihar Kanon ta haramta shiryawa da nuna fina-finan kwacen wayar salula, da shaye-shayen miyagun kwayoyi da garkuwa da mutane.

Shugaban hukumar tace fina-finan a Kano, Isma’ila Na’abba Afakallah ya shaida wa BBC cewa irin wadannan fina-finai na gurbata tarbiyar wadanda ke kallon su.

Afakallah ya ce kamata ya yi masu shirya fina-finan na Kanyywood su mayar da hankalinsu kan fina-finan da suka shafi rayuwar al’umma da bunkasa al’adun Hausawa da ci gaban matasa.

Related posts

Leave a Comment