Tsarin bada rancen wadda ke karkashin Shirin da bankin duniya ya bullo da shi mai lakabin ACReSAL domin tallafawa manoma da nufin dakile mummunan tasirin da sauyin yanayi ke yi ga tsarin noma da kiwo, muhalli da kuma albarkatun ruwa, nada nufin kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar mazauna karkara.
Jihohi 19 na arewacin Najeriya da yankin birnin tarayya Abuja ne za su ci gajiyar wannan Shirin na ACReSAL, amma shi wancan tsari na bada lamuni ga manoma a tafarkin da babu kudin ruwa a ciki.
An zabi jihohin Jigawa da Yobe ne domin kaddamar dashi a matakin gwaji, a cewar Alhaji Shehu Mohammed, Kodinetan dake kula da Shirin ACReSAL a jihar Yobe.
Ya kara da cewa, “Kowace kungiya za’a ba ta dala dubu 25, sai akace ayi gwaji, shine aka zabi jihohi 8 daga cikin 19 na arewa kuma sai aka fara aikin gwajin da jihohin Jigawa da Yobe kuma yanzu haka mun je mun zauna da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomin da za’a fara gwajin dasu kuma an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata”.
Dr Nura Ibrahim Kazaure dake zaman Kwamishinan Kula da Muhalli da Lamuran Sauyin Yanayi na jihar Jigawa yace gwamnatin jihar na daukar wannan shirin na Bankin Duniya da muhimmancin gaske, yana mai cewa
“Gwamnatin Jigawa tayi fice, har lambar yabo aka bamu a bara, saboda mu kadai ne jihar da suka sanya naira biliyan daya a matsayin namu kason na aiwatar da wannan Shirin kuma a bana ma muna nazarin adadin kudaden daya kamata mu zuba”
