Kamfanonin Jiragen Sama Sun Janye Matakin Tsunduma Yajin Aiki

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?ungiyar kamfanonin sufurin jiragen sama ta ce ta fasa dakatar da zirga-zirgar jiragen da ta yi niyyar yi daga yau Litinin.

Shugaban ?ungiyar Airline Operators of Nigeria (AON) Abdulmunaf Yunusa Sarina ne ya tabbatar wa BBC Hausa haka a ranar Lahadi cewa sun jingine matakin nasu.

Tun farko ?ungiyar ta ce za ta dakatar da aiki ne saboda tsadar man jirgi da ake sayarwa kan N700 a kowace lita.

Da ma rahotanni sun ambato wasu kamfanonin na cewa ba za su shiga yajin aikin ba kamar yadda ?ungiyar tasu ta nema. Kamfanonin Ibom da Dana na cikin wa?anda aka ambato na cewa za su ci gaba da aiki.

A ranar Asabar, gwamnatin tarayya ta ro?i kamfanonin da kada su dakatar da ayyuka “saboda zai shafi tattalin arzikin ?asa”.

Related posts

Leave a Comment