Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari na kan hanyar zuwa Abidjan babban birnin Ivory Coast domin halartar taron Majalisar ?inkin Duniya kan kare kare muhalli musamman yadda za a magance kwararowar hamada.
Sanarwar da fadar shugaban ta fitar ta ce Buhari zai bar Abuja a ranar Lahadi zuwa Abidjan, domin halartar taron na kwana biyu da za a soma a ranar Litinin.
Taron ya shafi yadda za a magance kwararowar hamada da fari da zabtarwar ?asa da sauran matsalolin muhalli, zai ?unshi shugabannin ?asashe da sauran masu ruwa da tsaki.
Buhari zai tafi tare da rakiyar ma?araban gwamnatinsa da suka ?unshi ministan harakokin waje Geoffrey Onyeama da na muhalli Mohammed H. Abdullahi da ministan noma Dr Mahmoud Mohammed da kuma na ruwa Inginiya Suleiman H. Adamu.
